Rundunar da ke kula da sha’anin tsaro ta gwamnatin Jihar Kuros Riba ta “Operation Akpakwu”, ta yi dirar mikiya kan wasu gidaje hudu da ake zargi mallakar wasu masu ta’adar garkuwa ne.
Rundunar ta yi rushe gidajen a yankin 8-Miles da ke birnin Kalaba, gidajen mallakar wasu mutane da Jami’an tsaro suka kama bisa zarginsu da laifin garkuwa da mutane.
- Jonathan zai jagoranci taron Daily Trust ranar Alhamis
- Yadda ’yan bindiga suka sace Farfesa suka harbi yaransa biyu a Zariya
Rundunar tsaron ta kuma rushe ginin wata mashaya da ke kusa da shatale-talen kamfanin Fulawa a birnin Calabar saboda zargin wurin a matsayin matattarar masu laifi da siyar da muggan kwayoyi.
Da yake gabatar da jawabi jim-kadan bayan gabatar da aikin rusau a ranar Litinin, mai ba gwamnatin jihar shawara kan sha’anin tsaro, Mista Henry Okokon, ya ce wannan aikin na daya daga cikin ayyukan magance ‘yan ta’adda a Jihar.
“Wannan jan kunne ne kuma izina ne ga dukkan mai sha’awar shiga ayyukan ta’addanci,” in ji Okokon.
Okokon, ya bukaci masu gudanar da kasuwanci a fadin jihar da su ci gaba da gudanar da harkokinsu kamar yadda suka saba, tare da cewa gwamnatin Jihar na iya bakin kokarinta na ganin ta kare su daga miyagun ‘yan ta’adda.
Kamfanin Jakadancin labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito cewa, rundunar ta Operation Akpakwu hadin gambiza ce da ta hada da Dakarun Sojin ruwa da na sama da ‘Yan sanda da Jami’an tsaron farin kaya.