Ma’aikatar Kula da Ayyukan Noma da Raya Karkara a Najeriya, ta rufe wasu kamfanoni hudu a Jihar Kano da ke hada takin zamani marasa inganci suna kuma sayarwa ba bisa ka’ida ba.
Kwamitin kar-ta-kwana na ma’aikatar ne ya gano kamfanonin tare da rufe su a Kananan Hukumomin Gwarzo da Dawakin Kudu da kuma Kumbotso na jihar.
- Barci ya kwashe wasu matukan jirgin sama a sararin samaniya
- Cutar zanzana ta jawo wa manoman Dankalin Turawa asara a bana
Yayin ziyarar da suka kai kamfanoni, ‘yan kwamitin sun gano cewa kamfanonin ba sa aiki bisa ka’ida, sannan su na kuma hadawa da wasu sinadarai marasa inganci a takin zamanin da suke sarrafawa su sayar wa jama’a.
A cewar Mista Oke Sunday, Darakta mai kula da ingancin takin zamani da sauran kayayyakin noma na ma’aikatar, wannan zagaye na sa ido ya zama dole ne, domin tabbatar da ana samar da takin zamani mai inganci ga manona.
A yayin zagayen ‘yan kwamitin sun gano tarin wasu sinadarai na hada takin zamani da aka haramta sayar da su a kasuwa.
‘Yan kwamitin sun kuma kama wata motar daukar kaya makare da takin zamanin na jabu a cikin zagayen na su.
“Za mu gurfanar da wadanda aka kama da haramtattun sinadaran hada takin zamani da zaran mun kammala cikkaken bincike” in ji Mista Oke.