✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta rage kudin mai

Da wannan sabon ragin, za a rika sayar da kowacce lita a kan N162.44 sabanin N168

Bayan fuskantar matsin lamba daga Gwamnatin Tarayya kan ta rage kudin mai, a karshe dai gwamnatin ta amince ta rage N5 a kan farashin kowacce lita.

Ministan Kwadago, Chris Ngige shine ya bayyana hakan bayan tattaunawar da gamayyar kungiyoyin kwadago a dakin taro na Fadar Shugaban Kasa dake Abuja.

Da wannan sabon ragin da zai fara aiki daga ranar 14 ga watan Disamban 2020, za a rika sayar da kowacce lita a kan N162.44 sabanin N168 da ake sayarwa yanzu haka.

An fara tattaunawar ne tun misalin karfe 8:55 na daren ranar Litinin har zuwa karfe 1:27 na safiyar ranar Talata.

Ngige ya ce tuni aka kafa wani kwamiti domin tabbatar an sami daidaito a farashin man.

“Tattaunawar mu da ‘yan kwadagon ta haifar da da mai ido, kasancewar Kamfanin Mai na NNPC wanda shine babban mai shigo da mai da ma sauran ‘yan kasuwa sun amince su rage N5 daga ranar Litinin mai zuwa,” inji Ngige.

Sai dai ministan ya ce rage farashin ba wai yana nufin an janye cire hannun gwamnati daga harkar mai ba ne saboda bai shafi farashin danyen mai ba.

Shi kuwa shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) Ayuba Wabba ya ce an cimma matsayar ne tare da amincewar duka bangarorin guda biyu.