✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta lashe amanta kan dawowar jiragen Daular Larabawa

Gwamnati ta ce zuwa yanzu babu ranar dawowar aikin kamfanonin jiragen Emirates da Etihad a Najeriya.

Gwamnatin Tarayya ta ce zuwa yanzu babu ranar da kamfanonin jiragen sama na Emirates da Etihad na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) za su ci gaba da aiki a Najeriya.

Murna ta koma ciki ne bayan a ranar Alhamis gwamnatin ta ce ba ta kammala cim-ma yarjejeniya da hukumomin UAE kan taƙaddamar Najeriya da hukumomin ƙasar kan sufurin jiragen sama ba.

Da farko, bayan tattaunawar Shugaba Bola Tinubu ranar Litinin da takwaransa na UAE, Sheik Mohamed bin Zayed Al Nahyan a birnin Abu Dhabi, hadimin shugaban kasa, Ajuri Ngelale, ya ce shugabannin biyu sun cim-ma yarjejeniya mai cike da tarihi, kan janye haramcin ba da bizar UAE ga matafiyan Najeriya.

Ya ƙara da cewa kamfanonin jiragen Emirates da Etihad kuma za su ci gaba da aiki a Najeriya.

Wata sanarwar gwamnatin UAE ta ce ita da Najeriya za su ci gaba da aiki domin karfafa dangantakarsu da nufin cin moriyar damar da suke da ita a tsakaninsu.

Amma kuma da yake magana a Abuja a wurin Babban Taron Sufurin Jiragen Sama na Afirka, Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya ce ba a kammala cim-ma daidito kan sharuddan yarjejeniyar ba.

“Muna kokarin kammala duk abubuwa da suka kamata, manya da kanana.

“Na tattauna da kamfanin Emirates a UAE kuma har yanzu muna kan tattaunawa, amma a yanzu ba za mu iya cewa ga lokacin da za a kammala ba.

“Fara sufurin jiragen sama ba abu mai sauƙi ba ne; ba kawai ɗaukar jirgi za a yi a fara ba, kusan sai an sake jadawalin zirga-zirgar kamfanin gaba daya da dai sauransu

“Sannan sai an an samu izinin hukumomin cikin gida da na kasashen waje.

“Amma dai na faɗa musu karara cewa ba za su nuna wa kamfanonin jiragenmu fifiko ba a yarjejeniyar,” in ji Keyamo