Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya ce Gwamnatin Tarayya ta ki daukar mataki a kan kisan da aka yi wa Fulani sama da 800 a Jihar Taraba duk da bayanan da ya mika mata a kan haka.
Sarkin Kanon ya tabbatar wa BBC cewa ya mika wa gwamnati hotunan Fulani 800 – cikinsu har da mata da kananan yara – da aka kashe a Jihar Taraba, amma har yanzu babu matakin da aka dauka.
Ya yi wannan bayani ne a daidai lokacin da ake zargin Fulani makiyaya da kisan mutane da dama a jihohin Benuwai da Taraba, zargin da Fulani makiyayan suka musanta.
Gwamnatin Tarayya ta sha musanta cewa sakacinta ne yake haifar da wannan rikici. Kuma a kwanakin baya Mai taimaka wa Shugaban kasa a fannin wasta labarai Malam Garba Shehu ya bayyana wa BBC cewa gwamnatin ta fara daukar hanyoyin kawo karshen rikicin baki dayansa.
A farkon makon nan ne Sufeton Janar na ’Yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris ya koma Jihar Benuwai bayan samun umarni daga Shugaban kasa kan hakan duk a kokarin kawo karshen rikicin.
Sai dai Sarkin Kano ya dora alhakin kashe-kashen da suke faruwa a jihohin a kan Fulani makiyaya da manoman jihohin, kuma ya koka kan yadda ba a bayar da hakikanin yawan Fulanin da aka kashe inda ake nuna bangaranci.
Sarki Sanusi, wanda ya tabbatar da hirar da ya yi da jaridar Punch kan lamarin, ya ce, “A ’yan watannin da suka gabata a Mambila, mayakan sa-kai na kabilun yankin sun kashe Fulani sama da 800. Babu jaridar da ta je can ballantana ta ba da labarin abin da ya faru.”
Ya ce, “Cikin mutanen da aka kashe har da wata mace mai ciki, wadda aka farke cikin nata aka fito da jaririn sannan aka yanka shi. Da kaina na mika wa Gwamnatin Tarayya wani kundi dauke da sunaye da hotunan mutanen da aka kashe da adireshin mutanen da ake zargi da yin kisan.”
Sarki Sanusi ya ce, “Kazalika, sai da na tabbata cewa hukumomi sun karbi shaidun bidiyo da hotuna na manyan ’yan siyasar Jihar Taraba wadanda suke da hannu a wannan kisa na kare-dangi. Amma babu wanda aka kama. An kashe Fulani a Kajuru (Jihar Kaduna) da Numan (Jihar Adamawa). A lokuta da dama mayakan sa-kai ne kawai ke dirar wa Fulanin su kashe mata da ’ya’yansu.”
Ya kara da cewa irin wannan rikicin ba zai kare ba idan ba a dauki mataki a kan mutanen da ke haddasa su tun da farko ba.