✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta kara wa’adin hutun dalibai a Kano

Gwamnatin Kano ta tsawaita wa’adin komawar daliban makarantun Firamare da Sakandire bayan hutun karshen zangon karatu na farko da suka tafi makonni biyu da suka…

Gwamnatin Kano ta tsawaita wa’adin komawar daliban makarantun Firamare da Sakandire bayan hutun karshen zangon karatu na farko da suka tafi makonni biyu da suka gabata.

Sanarwar da Kwamishinan Ilimi na Jihar, Malam Sanusi Muhammad Kiru ya raba wa manema labarai, ta ce an kara wa’adin komawa makarantun ne da mako guda.

Sanarwar ta ce, makarantun kwana za su koma a ranar Lahadi, 18 ga watan Afrilun 2021 yayin da kuma na ’yan jeka-ka-dawo za su koma a ranar Litinin, 19 ga watan Afrilun na bana.

A cewarsa, matakin tsawaita wa’adin komawar daliban ya biyo bayan gabatowar watan Azumin Ramadana, domin bai wa iyaye damar gudanar da shiri cikin tsanaki.

A baya dai gwamnati ta sanya ranar Litinin, 12 ga watan Afrilun 202, a matsayin ranar komawar dalibai a fadin jihar.