✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta kafa dakarun kare albarkatun noma

Gwamnatin Tarayya ta kafa jami’an tsaro na musamman da za su rika ba da kariya ga dukiyar da aka zuba a bangaren harkokin noman kasar.…

Gwamnatin Tarayya ta kafa jami’an tsaro na musamman da za su rika ba da kariya ga dukiyar da aka zuba a bangaren harkokin noman kasar.
Dakarun za su rika yaki da satar shanu da rikicin manoma da makiyaya da ke aukuwa a sassa da dama na kasar.
Matimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ne ya yi bayyanin a taron kwanaki uku da aka yi kan yadda za a farfado da kamfanonin bunkasa kiwo wanda aka gudanar a Abuja, jiya.
Osinbajo wanda Ministan Albarkatun Noma, Dokta Audu Ogbeh, ya bayyana cewa tuni gwamnati ta bayar da horo ga dakaru dubu uku don magance satar shanu tare da kare albarkatun noma.