Gwamnatin Zamfara ta tabbatar da mutuwar fararen hula a luguden wuta da jiragen yaki suka yi kan ’yan bindiga a jihar.
Gwamnan Bello Mohammed Matawalle ya tabbatar da hakan ne a yayin ta’aziyyarsa bayan luguden wutan da jiragen yaki suka yi kan maboyar ’yan bindigar a Karamar Hukumar Maru ta jihar.
“Wannan abin ya faru ne a yayin da gwamnatin jihar da sojoji suka zage damtse domin murkushe ayyukan ’yan bindiga gaba daya, ta hanyar fatattakar su har a zuwa maboyarsu,“ in ji gwamnan.
Matawalle ta hannun kakakinsa, Zailani Bappa, a ranar Talata, ta bayyana alhininsa bisa mutuwar fararen hula da ba su ji ba, ba su gani ba, a yayin da jiragen yakin ke yi wa bata-garin luguden wuta.
“Ni da iyalaina da gwamnati da daukacin al’ummar Jihar Zamfara na jajanta wa wadanda suka samu rauni da kuma iyalan wadanda suka rasu a wannan al’amari,” in ji shi.
A cewarsa, gwamnatin ta dauki matakin magance aukuwar irin matsalar a nan gaba.