Gwamnatin tarayya ta dakatar da shugaban kwamitin bincike na musamman kan kwato kadarorin gwamnati, Cif Okoi Obonono-Obla kan zargin rashin bin ka’ida.
A wata wasika mai lamba: HAGF/SH/2017/VOL/1/60 mai dauke da kwanan watan ranar 1 ga watan Nuwamban shekarar 2017 wacce Atone Janar na kasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya sanya wa hannu ya ce an zargi Obla da wani laifi wanda ya saba wa ka’idar aikinsa.
An ummarci Obla ya wanke kansa a wajen Atone Janar kafin ya yi hira da wata kafar yada labarai ko kuma fitar da wata sanarwa.