✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnati ta dakatar da ayyukan shafin Twitter a Najeriya

Hakan na zuwa ne bayan kwanaki da shafin ya goge wani sakon Buhari.

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da ayyukan shafin zauren sada zumunta na Twitter a Najeriya.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Ministan Labarai da Al’adu na Kasar, Alhaji Lai Mohammed ya fitar a ranar Juma’a.

Sanarwar mai dauke da sa hannun Segun Adeyemi, Hadimi na musamman ga Ministan kan Harkokin Sadarwa, ta ce ana ribatar shafin na Twitter wajen kawo rabuwar kai a kasar nan.

Kazalika, sanarwar ta bai wa Hukumar Kula da Ayyukan Gidajen Rediyo da Talbijin ta Kasa (NCC) ta fara shirye-shiryen ba da lasisi ga kafafen yada labarai na intanet.

Wannan mataki na zuwa ne kwanaki kadan bayan da shafin Twitter ya goge wani sako na gargadin ’yan awaren IPOB da Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa.