Gwamanatin Najeriya ta cire hannunta daga sanya farashin man fetur, inda ta mika wa ’ya kasuwa wuka da naman cinikinsa da shigo da shi da kuma sanya farashin sayar da shi ga ’yan kasar.
Hukumar Kayyada Farashin Albarkatun Mai (PPPRA) ta ce gwamnati ta cire hannunta gaba daya a harkar shigo da mai, don haka ba ruwanta da alhakin sanya farashinsa.
- Mutum shida ’yan gida daya sun mutu a ambaliya
- ’Yan bindiga 200 sun mika wuya a Sakkwato
- ‘Ma’aikatun gwamantin Najeriya sun yi watanda da Naira tiriliyan 1.2‘
Sanarwar janye hannun gwamna na samun mabambantan sharhi daga masana da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren a kan tasirin matakin ga tattalin arzikin kasar.
Wasu na ganin sabon matakin zai kara tsadara albarkatun mai, wasu kuma na ganin farashin zai ragu a hankali kamar yadda ya faru bayan gwamnati ta cire hannunta a bangaren sadarwa.
Akwai kuma masu ganin cewa babu amfanin da talakan Najeriya zai samu daga cire hannnun gwamnatin muddin ba a cikin kasar a ke tace mai ba.
A ranar 2 ga Satumba, 2020 Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC) ta bakin PPMC mai kula da albarkatun mai ya kara farashin sayar da fetur ga manyan dillalai daga N138.62k zuwa N151.56k.
Sakamakon haka farashinsa a gidajen mai ya karu zuwa tsakanin N160 da N163 a fadin kasar.