Gwamnatin Tarayya ta cire dokar nan ta hana fita ta tsakar dare da kuma taruwar jama’a a tarukan bikin aure da na nishadi wadanda aka saka da zimmar yaki da annobar Coronavirus.
Kwamatin yaki da cutar na shugaban kasa wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ke jagoranta, ya ce an dauki matakin ne sakamakon raguwar mutanen da ke kamuwa da cutar a kasar.
- Za a yi wa Blaise Compaore daurin rai-da-rai saboda kashe Thomas Sankara
- Wani mutum ya rataye kansa a Kano
Wannan dai na zuwa ne yayin da a ciki wata sanarwa daga kwamitin ta ce an kuma samu raguwar hadarin yada sabon nau’in cutar na Omicron.
Sai dai kuma, ya jaddada cewa wajibi ne mutane su ci gaba da saka takunkumi idan suna cikin wani rufaffen wuri amma bai zama lallai su saka ba idan suna budadden wuri ko kuma fili.
An janye kayyadewar adadin mutanen da za su halarci wani taron addini amma kwamatin ya ce lallai ne a saka takunkumi a wurin.
Ana iya tuna cewa, a tun bayan bullar annobar Coronavirus ce Kwamitin ya sanya dokar a wani yunkuri na dakile yaduwar cutar a fadin kasar.