✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta biya N708m haƙƙoƙin tsoffin ma’aikata 461 a Yobe

Ba shakka biyan haƙƙoƙin zai tallafa wa rayuwar wadanda suka yi ritaya.

Gwamna Mai Mala Buni ya amince da biyan Naira miliyan 708 a matsayin haƙƙoƙin ma’aikata 461 da suka yi ritaya a fadin Jihar Yobe.

An amince da biyan tsoffin ma’aikatan haƙƙoƙin su ne bayan kammala tantance kashi na uku na masu karbar fansho a kananan hukumomi 17 na jihar da aka yi.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun gwamnan, Mamman Mohammed, ya ce za a biya wadanda suka yi ritaya ne kai tsaye yayin da ’yan uwan wadanda suka rasu za su karbi haƙƙoƙin a madadinsu.

“Ba shakka biyan haƙƙoƙin zai tallafa wa rayuwar wadanda suka yi ritaya, musamman ma ga  rayuwa irin na wadanda suka daina aiki.”

“Za a iya tunawa cewa a watan Nuwambar shekarar da ta gabata ne Gwamna Buni ya amince da sake nazari kan batun biyan kudaden giratuti wanda aka kara daga Naira miliyan 100 zuwa Naira miliyan 200 duk wata.”

Gwamnan ya ce sake nazari kan kudaden na da nufin kara yawan masu cin moriya duk wata.

Binciken ya kuma ba da damar tabbatar da ci gaba da biyan fanshon ma’aikatan da suka yi ritaya a kan lokaci don tallafa wa rayuwarsu a lokacin ritaya.