✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta ayyana hutun Karamar Sallah a Najeriya

Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis.

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin da Talata na makon gobe a matsayin ranakun hutun bikin Karamar Sallar bana.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis.

“Litinin 2 da Talata 3 ga watan Mayun bana su ne ranakun hutun da Gwamnatin Tarayya ta bayar domin bukukuwan Sallah Karama a bana,” a cewar sanarwar.

“Ina kiran Musulmi da su yi koyi da kyawawan dabi’u na Manzon Allah (S.A.W), wajen yi wa juna alheri, nuna kauna da sadaukarwa.

“Sannan su yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa kasar nan addu’o’in zaman lafiya, hadin kai, ci gaba da samun kwanciyar hankali a kasar duba da kalubalen tsaron da muke fuskanta a wannan lokaci.”

Cikin sanawar mai dauke da sa hannun Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Wajen, Dokta Shu’aib Belgore, Aregbesola ya taya Musulmi murnar kammal Azumin watan Ramadan da kuma zuwan Sallar.

Haka kuma, ya bai wa dukkanin mazauna kasar nan tabbacin cewa gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a tsaye take kyam wajen ganin ta tsaye rayuka da dukiyar al’umma.

Ya kuma tunatar da ’yan Najeriya cewa tilas ne sai da hadin kansu za a samar da tsaro da aminci musamman ta hanyar sanya idanun lura da shigar da rahoton duk wani motsi da ba su aminta da shi ba ga mahukuntan da suka dace.