Gwanmatin Tarayya ta ayyana Talata da Laraba na makon gobe a matsayin ranakun hutun bikin Babbar Sallar bana.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya sanar da hakan a ranar Alhamis.
“Talata 20 da Laraba 21 ga watan Yulin bana su ne ranakun hutun da Gwamnatin Tarayya ta bayar domin bukukuwan Sallah Babba a bana,” a cewar sanarwar.
“Ina kiran Musulmi da su yi koyi da kyawawan dabi’u na Manzon Allah (S.A.W), wajen yi wa juna alheri, nuna kauna da sadaukarwa.
“Sannan su yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa kasar nan addu’o’in zaman lafiya, hadin kai, ci gaba da samun kwanciyar hankali a kasar duba da kalubalen tsaron da muke fuskanta a wannan lokaci.”
Cikin sanawar mai dauke da sa hannun Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Wajen, Dokta Shu’aib Belgore, Aregbesola ya taya Musulmin murnar zuwan Sallar.
Tun a makon da ya gabata ne Mai Alfarma, Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya sanar cewa a ranar Talatar makon gobe za a yi bikin Babbar Sallah a bana bayan bayyana jinjirin watan Zhul Hajj.
Ranar Litinin, 19 ga Yulin 2021, ita ce 9 ga watan Zhul Hajj na shekarar 1442 Hijiriyya, wadda ita ce ranar da za a yi hawan Arfah ga Mahajjata masu gudanar da Aikin Hajji a bana a kasa mai tsarki.
Washegari Talata ce za ta kasance ranar Idin babban Sallar bana.