✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta amince da bukatar kungiyar kwadago kan albashi

Shugaban kungiyar kwadago NLC ta Najeriya Ayuba Wabba ya ce, gwamnatin tarayya kwanan zata sanar da sabon albashi mafi karanci ga ma’aikatan kasar. Shugaban ya…

Shugaban kungiyar kwadago NLC ta Najeriya Ayuba Wabba ya ce, gwamnatin tarayya kwanan zata sanar da sabon albashi mafi karanci ga ma’aikatan kasar.

Shugaban ya bayyana hakan ne, bayan kammala ganawar kwamitin wanda zasu mika shi ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari don samun amincewarsa.

Wabba ya sanar da hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a Abuja.