✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnati na son cire ’yan Najeriya miliyan 40 daga talauci cikin shekara 2

Gwamnatin ta ce za ta yi hakan ne ta hanyar shirinta mai suna NG-CARES

Gwamnatin Tarayya ta ce ta fara yunkurin cire ’yan Najeriya miliyan 40 daga kangin talauci nan da shekara biyu masu zuwa.

A cewarta, za ta yi hakan ne ta hanyar shirinta na farfado da tattalin arziki da rage radadin talauci bayan annobar COVID-19 mai suna NG-CARES.

Jami’in shirin na kasa, Abdulkarim Obaje, ne ya bayyana hakan a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo ranar Lahadi, yayin bikin rufe wani taron kara wa juna sani kan shirin.

An dai gudanar da taron ne a Ibadan, kuma ya samu halartar mutum 440 daga Jihohi 36 da ma Babban Birnin Tarayya Abuja.

Daga cikin wadanda aka horar din har da wadanda za su rika kula da shirin a sassa daban-daban na Najeriya.