✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati na kashe $10m wajen ciyar da dalibai miliyan 10 —Ngige

Wannan wani yunkuri ne na karfafa gwiwar yaran don mayar da hankali a karatu.

Gwamnatin Tarayya ta ce tana kashe dalar Amurka miliyan 10 a karkashin shirinta na ciyar da yara ‘yan makarantun firamare miliyan 10 da ke sassan kasar.

Gwamnatin ta ce tana kashe wannan tsabar kudi ne a matsayin wani yunkuri ne na karfafa gwiwar yaran don mayar da hankali a karatu.

Ministan Kwadago da Samar da Ayyukanyi na Najeriyar, Chris Ngige ne ya sanar da wannan alkaluman yayin karbar bakuncin Jakadar Amurka a Najeriya, Mary Leornard a ofishinsa da ke Abuja.

Mininistan ya ce Gwamnatin Najeriya ta samar da shirin ciyar da yara a makarantu ne don magance bautar da su a zamanance da ake yi da sunan aikatau ta hanyar mayar da su makarantu.

Ngige ya ye gwamnati ta samar da shirye-shiryen ne domin yaki da talauci, da kuma kwadaitar da yara karatu baya ga kawar da matsalar bautarwa ga yaran musamman a karkara.

Ministan ya ce a yanzu akwai yara ‘yan makaranta kimanin miliyan goma da ke cin gajiyar wannan shirin a sassan Najeriya musamman a yankunan karkara.