Yayin da babbar kungiyar ’yan adawar kasar Chadi ta bijire wa sulhu da gwamnatin sojin kasar, sauran kungiyoyin su 40 sun rattaba hannu kan yarjejeniyar a kasar Qatar.
A karkashin yarjejeniyar dai wacce aka kulla a birnin Doha babba birnin kasar, an cim ma matsaya kan zaben Shugaban Kasa da za a fara gudanarwa ranar 20 ga watan Agustan nan mai zuwa.
Tun a watan Maris ne dai Qatar din ta fara shiga tsakanin kungiyoyin adawar da gwannatin sojin ta Mahamat Idris Deby Itno, da ya kwaci mulkin kasar bayan rasuwar mahaifinsa a hannun ’yan tawaye a 2021.
To sai dai babbar kungiyar adawar Chadin ta FACT ta ce ba za ta sanya hannu kan yarjejeniyar ba, duk da ban bakin da Qatar din ta yi mata.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a Doha kafin sanya hannu kan yarjejeniyar, FACT din ta ce ba ta amince da yarjejeniyar ba, tare da bukatar kafa wani kwamitin da zai shirya sabuwar tattaunawa da kuma sakin ’yan tawayen da ke kulle a gidajen yarin kasar.
Kungiyar ta FACT din mai mayaka fiye da 1,500, ta ce a shirye take domin bude sabuwar tattaunawa a kowanne lokaci.
Kungiyar dai ita ce ta jagoranci yakin da mahaifin Deby wato shugaban kasar Chadin da ya shafe shekaru 30 kan karagar mulki ya rasa ransa.