✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnan Sokoto ya yi ganawar sirri da Obasanjo

Gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal ya yi ganawar sirri da tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo a Abeokuta

Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya yi ganawar sirri da tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo a garin Abeokuta na Jihar Ogun.

Kakakin Obasanjo, Kehinde Akinyemi ya ce Tambuwal ya ziyarci Obasanjo ne a ranar Asabar domin neman shawarwari a kan al’amuran shugabanci da sauran matsaloli.

Takardar da ya fitar ta ambato gwamnan na cewa Obasanjo, “Shugabanmu ne kuma dattijo, don haka yana da kyau mu ziyartarsa mu gaishe shi tare da duba lafiyarsa sannan mu nemi shawarwari gwami da batutuwan shugabanci jefi-jefi”.

Ya ce gwamnan ya nuna jin dadi da ganin Obasanjo cikin koshin lafiya da walwala.

“Za mu ci gabda da daukar darasi daga gare shi da kuma kwarewa da hikima da tarin iliminsa kan abubuwan shugabanci na wannan zamani”, inji shi.

Game da matsalolin Jihar Sokoto, Tambuwa ya ce, “Muna kokarin samar da zaman lafiya a jihohin Arewa inda ake fama da matsalolin ‘yan bindiga.

“Aminci na samuwa, mutane na komawa gonakinsu da kauyukansu daga sansanonin gudun hijira.

“Muna yin iya kokarinmu a matsayin gwamnatocin jihohi wajen ganin tsaro ya samu da ci gaban al’umma da samuwar ayyuka.”