Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu ya raba gero ga iyalan wadanda harin ’yan bindiga na ranar Lahadi ya shafa.
Gwamnan ya kuma ba da tallafin kudi ga wadanda suka samu rauni ko rasa wata kadara a lokacin harin.
A satin da ya gabata ne ’yan bindiga suka kai hari a wasu kauyukka biyar a Karamar Hukumar Tangaza inda suka kashe mutum 37, wasu da dama suka samu rauni.
Gwamna Ahmad Aliyu ya ziyarci mutanen ne tare da rakiyar mataimakinsa, Idris Muhammad Gobir da Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar da jagoran jam’iyar APC a Sakkwato, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko wanda ya baiyana harin da cewa rashin hankali ne da dakikanci.
- Dan shekara 38 ya zama shugaban majalisar Osun
- DAGA LARABA: Yadda Cire Tallafin Mai Ya Shafi Rayuwarmu —’Yan Najeriya
Ya bai wa mutanen jihar tabbacin gwamnati ba za ta huta ba har sai ta kare rayuwar mutane da dukiyoyinsu.
“Za mu yi duk abin da muke iya yi na ganin an kawo karshen wannan kashe-kashen na rashin hankali,” a cewarsa.
Ya roki Allah da Ya gafarta wa wadanda suka rasu, Ya ba wadanda suka samu rauni lafiya.
A cewarsa, ma akwai bukatar mutanen kauyen su kai duk wani rahoton abin da ba su gamsu da shi ba a cikin al’ummarsu ga jami’an tsaro.
Ya yi kira gare su da su hada kai da jami’an tsaron da aka kai masu domin samar musu da zaman lafiya.