Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya haramta sana’ar karuwanci da fatin dare, wato ‘night club’ a Fatakwal, babban birnin Jihar.
Gwamnan ya ba da umarnin ne a sakonsa na sabuwar shekara ga al’ummar Jihar ranar Asabar.
- ‘Sata muke yi da karuwanci mu samu kudin shaye-shaye a Sabon Gari’
- Ba zan ci gaba da fitowa a shirin ‘Labarina’ ba – Nafisa Abdullahi
A cewarsa, dokar ta shafi haramta fatin ne da kuma sana’ar karuwanci, musamman a kan titin Abacha da yankin unguwar Casablanca.
Gwamnan ya ce, “Matakin zai hana gurbacewar tarbiyyar kananan yara da ma ta al’umma baki daya.
Sai dai bai fadi tsawon wane lokaci haramcin zai dauka ba.
Wike ya kuma umarci jami’an tsaro a jihar da su kama tare da gurfanar da duk wanda ya karya dokar a gaban kotu.
Ya ce za a kafa kwamitin kar-ta-kwana don tabbatar da bin dokar.
Wa’adin gwamnan dai zai kare ne bayan kakar zabukan shekara ta 2023.