Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya yi wa al’ummar Arewa da ke zaune a jihar ta’aziyyar rasuwar Limamin Babban Masallacin Juma’a na Unguwar Sabo Ibadan, Sheikh Ahmad Rufa’i Hussaini.
Marigayin ya rasu ne cikin daren Asabar a gidansa da ke Sabo bayan gajeruwar rashin lafiya, yana da shekaru 72.
A cikin sakon ta’aziyar da ya aika wa Sarkin Hausawan Ibadan Alhaji Ahmad Dahiru Zungeru ranar Lahadi, gwamnan ya ce marigayin jagora ne wajen ciyar da al’umma gaba.
“Marigayi Sheikh Rufa’i Hussaini ya samu kyakkyawar shaida a kan fafutukar ganin ci gaban al’ummarsa ta fannin yada manufofin addinin Musulunci a tsakanin al’ummar musulmin jihar baki daya ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba,” inji sanarwar, wadda mataimaki na musamman ga gwamnan a kan al’amuran jaridu, Mista Moses Alao, ya sanya wa hannu.
- Mace-macen Hadejia ba su da nasaba da COVID-19 –Kwamitin bincike
- Alkalin da ya soke zaben Abiola ya rasu
Sarakunan Hausawa da manyan malaman addinin Musulunci na ciki da wajen Ibadan tare da dimbin jama’arsu ne suka halarci sallar jana’izar da Sheik Ibrahim Inuwa ya jagoranta a harabar Babban Masallacin Juma’a na Unguwar Sabo, mazaunin Hausawa a birnin.
Sheikh Sa’adu Abubakar, Na’ibin Liman a masallacin, ya shaidawa Aminiya cewa, “mun yi babban rashin wannan bawan Allah da ya sadaukar da rayuwarsa baki daya wajen fafutukar tsayar da kalmar Allah (SWT) ba tare da kwadayin abin duniya ba.”
Daya daga cikin dattijan gari, Alhaji Aminu Yahya, cewa ya yi, “marigayi Liman yana daga cikin mutanen da suka shafe shekaru suna fafutukar kare martabar makabartu uku mallakar Hausawan Ibadan da wasu suke hada kai da mahukunta domin kwace su daga hannun mu.”
Shi kuwa babban yayan marigayin, Alhaji Musa Hussaini, cewa ya yi “Sheikh Ahmad Rufa’i Hussaini ya samu wannan kyakkyawar shaida ne daga irin tarbiyar da muka samu daga iyayenmu.”
Shi ma limamin Masallacin Darud Da’awa na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Ikamatis Sunnah a Ibadan, Sheikh Sani Haruna, rokon Allah ya yi Ya kai rahama kabarin marigayin musamman a kan halayensa na gudun duniya.
Marigayi Sheikh Ahmad Rufa’i Hussaini ya shafe shekaru 31 yana limancin wannan masallaci wanda shi ne masallaci na biyu mafi girma a Ibadan bayan babban masallacin dake tsakiyar garin.