Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya kalubalanci kungiyar kwallon Gora ta Niger Flickers da ke wakiltar Najeriya a gasar kwallon Gora ta Afirka da ake fafatawa a kasar Zambiya su yi kokarin lashe kofin Nahiyar Afirka a bana.
Gwamna Abubakar Sani Bello wanda ya nemi haka a wata takarda da Kakakinsa Malam Jibrin Baba Ndace ya sanya wa hannu ya ce babu shakka idan kungiyar ta yi rawar gani wajen lashe kofin za ta daukaka martabar Jihar Neja da kuma Najeriya a idon duniya.
Gwamnan ya zanta da ’yan wasan da jami’ansu ta waya, inda ya nanata cewa, wannan wata dama ce da za su yi amfani da ita wurin nuna kyawawan dabi’unsu da za su taimaka wurin dawo da martabar wannan kasa a idon duniya.
Ya tabbatar musu cewa tuni ya yi musu tanadi kan hakkokinsu, kuma za a tabbatar ya shiga hannunsu. Ya ce rashin biyan ’yan wasa hakkokinsu yadda ya kamata yana kawo matsala wadda takan yi tasiri a kowace gasa, don haka ya dauki matakin hana aukuwar haka.
Shugaban kungiyar kwallon Gora ta Najeriya reshen Jihar Neja, Alhaji Muhammad Sani Idris Kutigi ya yi wa Gwamnan godiya da ya dauki nauyin horar da su a horo na musamman da suka samu wanda hakan ya taimaka wa ’yan wasan wurin kara samun kwarewa da gyara kura-kuren da suke yi a yayin wasa.
Alhaji Sani Idris Kutigi ya yi wa Gwamnan alkawarin mika masa kofin kasancewa zakarun Nahiyar Afrika don kuwa sun san irin tanadin da suka yi wa gasar. Ya ce goyon bayan da jihar ta ba su ya kara musu azamar yin wasa yadda ya kamata.
Gwamnan Neja ya kalubalanci kungiyar kwallon Gora ta Niger Flickers
Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya kalubalanci kungiyar kwallon Gora ta Niger Flickers da ke wakiltar Najeriya a gasar kwallon Gora ta Afirka…