✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Kano ya raba wa alhazan Jihar miliyan 65 na ‘Barka da Sallah’

An ba alhazan sama da su 6,000 da yanzu haka ke Saudiyya ne tallafin

Gwamnatin Jihar Kano ta raba wa alhazain Jihar da yanzu haka ke kasar Saudiyya Naira miliyan 65 a matsayin barka da Sallah.

A cewar gwamnatin, kyautar wani bangare ne na kyautata wa alhazan don ganin sun ji dadin zamansu a kasar mai tsarki.

Hukumar da ke Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta sami kujeru dubu 95 inda Jihar Kano ta zama Jihar ta biyu da ke da mafi yawan alhazai har su 6,179.

Yayin da yake zantawa da manema labarai bayan wani taro da ya gudanar da jami’an alhazai na Kananan Hukumomi 44 da ke Jihar, Darakta Janar na Hukumar Jin dadin Alhazai na Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya ce Gwamnan ya ga dacewar a tallafa wa alhazan jihar wadanda a halin yanzu ke gudanar da ibada a kasa mai tsarki.

Danbappa ya kara da cewa kowane Alhaji ya sami Riyal 50, kwatankwacin Naira dubu 10.

Ya kuma yi kira ga alhazan da su yi amfani da kudin guzurinsu da kuma barka da Sallar da aka ba su ta hanyar da ta dace, su kuma guji yin almubazzaranci, lamarin da ka iya kawo musu matsala kafin komawarsu gida.

Ya kuma roki alhazan da su ci gaba da nuna halin da’a a yayin da suke zaune a kasa mai tsarki domin kare martabar jiharsu da kuma kasa Najeriya gaba daya.

Danbappa ya bayyana cewa jigilar alhazai don komawa gida za ta kasance ne kamar yadda alhazan suka je kasa mai tsarki, wato wanda ya riga zuwa shi zai riga komawa.

Don haka ya nemi alhazan da su yi hakuri har zuwa lokacin da za a kammala kwashe su zuwa gida.

Alhazan da suka zanta da Aminiya sun nuna jin dadinsu game da kyautar, inda suka yi fatan samun zaman lafiya da bunkasar arziki ga jihar.