Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi wa majalisar zartarwarsa garambawul, inda ya sallami Sakataren Gwamnati da Shugaban Ma’aikatan gwamna da Kwamishinan yaɗa labarai da wasu Kwamishinoni huɗu.
A cewar mai magana da yawun Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, wannan matakin wani ɓangare ne na wani ƙudurin siyasa don aiwatar da tsarin siyasar gwamnatinsa.
- ‘Yan sanda sun kama ɓarayin da ake zargi 7 da ƙwato motoci 13 a Abuja
- ‘Yan ta’adda 129,417 sun miƙa wuya ga sojoji cikin watanni shida – Janar Musa
A cewar sanarwar ta Sanusi Bature, Gwamna Abba Yusuf ya ci gaba da ɗaukar matakin garambawul ne don samar da kyakkyawan aiki wanda zai samar da romon dimokuraɗiyya ga mutanen jihar Kano.
Waɗanda sallamar ta shafa sun haɗa da Shugaban ma’aikatan Gwamnatin jihar, Alhaji Shehu Wada Sagagi da kuma Sakataren gwamnatin jihar, Dakta Abdullahi Baffa Bichi wanda aka sauke a dalilin rashin lafiya.
A cewar Bature, Gwamna Yusuf ya tsige wasu daga cikin jami’an gwamnatin, ya kuma sake naɗa wasu shugabannin ma’aikatu domin inganta ayyukan gudanar da harkokin mulki da na siyasa.
Waɗanda suke riƙe muƙaman su ne: Babban Alƙali kuma Kwamishinan Shari’a, Barista Haruna Isa Dederi, Kwamishinan Noma, Dakta Danjuma Mahmoud da Kwamishinan Lafiya, Dakta Abubakar Labaran da Kwamishinan Ƙasa da tsare-tsare, Hon. Abduljabbar Mohammed Umar, Kwamishinan kasafi da tsare-tsare Hon Musa Suleiman Shanono da Kwamishinan Ayyuka da gidaje Injiniya Marwan Ahmad.
Sauran da suke riƙe da muƙaman sun haɗa da: Kwamishinan albarkatun Ƙasa da ma’adinai, Sefiyanu Hamza, Kwamishinan harkokin addini, Sheikh Ahmad Tijani Auwal, Kwamishinan matasa da wasanni, Hon. Mustapha Rabiu Kwankwaso, Kwamishinan Zuba Jari da Kasuwanci, Adamu Aliyu Kibiya da na Tsaron Cikin Gida da Ayyuka na Musamman, Manjo Janar Mohammad Inuwa Idris (mai ritaya).