✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Kaduna ya yi sabbin nade-nade

Gwamnan ya bukaci wadanda aka nada su yi aiki tukuru don sauke nauyin da ya rataya a kansu.

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da nadin shugabannin hukumomi, masu ba da shawara na musamman da sauran manyan mataimaka a Jihar.

Shugabannin hukumomin uku sun hada da Mohammad Sada Jalal, Shugaban Hukumar Tattara Bayanan Filaye ta Jihar (KADGIS); Adamu Magaji, Darakta Janar na Hukumar Kula da Kadarorin Gwamnati ta Jihar (KADFAMA); Jerry Adams, Shugaban riko na Hukumar Tattara Harajin ta Jihar (KADIRS).

Jerry Adams zai yi aiki a matsayin Shugaban riko har sai an nada sabon Shugaban Hukumar.

Muhammad Lawal Shehu, Sakataren Yada Labarai na Gwamnan ne ya bayyana nade-naden a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Sauran wadanda aka nada sun hada da Adamu Samaila, mai ba da shawara na musamman kan harkokin kwadago; Amina Sani Bello, Babbar Mataimakiya ta Musamman kan Al’amuran Dalibai; Salisu Ibrahim Garba, babban mataimaki na musamman kan harkokin siyasa; Larai Sylvia Ishaku, Babbar Mataimakiya ta Musamman, Shirin Zuba Jari na Jama’a; Clement Shekogaza Wasah, Babban Mataimaki na Musamman, Hadin Kan Al’umma; da Waziri Garba babban mataimaki na musamman kan harkokin mulki.

Sanarwar ta ce, an yi nadin ne bisa la’akari da bayanan da aka samu na wadanda aka nada, da jajircewarsu wajen yi wa jihar Kaduna hidima.

Gwamnan ya taya daukacin wadanda aka nada murna, sannan ya bukace su da su yi aiki tukuru don sauke nauyin da aka dora musu.