Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya a ranar Talata ya amince da nadin Shugabannin rikon kwarya a Kananan Hukumomi 11 na jihar.
Sanarwar da ke dauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ta ce nadin nasu ya fara aiki ne nan take.
- Yadda gidan talabijin a Turkiyya ya kwashe ma’aikatan BBC Hausa guda 9
- Kotu ta yi sammacin Emefiele kan karar da ke neman tsare shi
Shugabanin Kananan Hukumomin da aka nada din su ne Alhaji Abubakar Usman Barambu na Karamar Hukumar Akko da Garba Umar Garus na Balanga, sai Margret Bitrus ta Billiri, da Alhaji Jamilu Ahmed Shabewa na Dukku, da Ibrahim Adamu Cheldu na Karamar Hukumar Funakaye.
Sauran sun hada da Aliyu Usman Haruna na Karamar Hukumar Gombe da Faruk Aliyu Umar na Kaltungo da Ibrahim Buba na Kwami da Salisu Shu’aibu Dendele na Nafada sai Yohanna Nahari na Shongom sai Garba Usman na karamar hukumar Yamaltu Deba.