✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnan Filato ya kamu da cutar coronavirus

Gwamna Lalong ya killace kansa bayan kamuwarsa da cutar coronavirus

Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato ya harbu da cutar coronavirus, a yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan karuwar cutar a karo na biyu.

Daraktan Yada Labaran Gwamnan, Makut Simon Macham, ya ce gwamnan ya killace kansa bayan da sakamakon gwaji ya nuna ya kamu da cutar.

“Sakamakon haka, Gwamna zai rika aiki ne daga gida a tsawon lokacin da yake da killace. Duk sha’anin aiki da ke bukalar ya hallara a zahiri kuma, Mataimakin Gwamna zai kula da su”, inji Makut.

Sai dai ya yi bayani cewa sakamakon gwajin da aka yi wa iyalan gwamnan ya nuna ba sa dauke da kwayar cutar ta coronavirus.

Ya ce duk da cewa alamun cutar ba su bayyana a zahirance a tare da gwamnan ba, yanzu haka an yi wa hadimansa da sauran makusantansa gwaji, ana kuma jiran sakamako domin tabbatar da yanayin lafiyarsu.

Lalong ya yi kira ga jama’ar jiyar da su kasance masu kiyaye matakan kariyar cutar coronavirus musamman a lokacin bikin Kirsimeti da Sabuwar Shekara, domin har yanzu cutar na nan tana bazuwa.