Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato, ya dakatar da wasu kwamishinoni biyu masu ci da wasu hadimansa.
Mutfwang, ya sanar da dakatarwar ne a wata sanarwa da Mista Gyang Bere, daraktan yaɗa labaransa, ya fitar a ranar Talata a Jos.
- Zulum ya raba wa magidanta 10,000 kayan abinci da 150m a Borno
- Ambaliyar ta hallaka mutum 30, 9,366 sun rasa muhalli a Jigawa
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN), ya ruwaito cewa jami’an gwamnatin da aka dakatar sun haɗa da Mista Chrysanthus Dawm da Misis Jamila Tukur, kwamishinonin kasafin kuɗi da tsare-tsare da na yawon buɗe ido da al’adu.
Sauran waɗanda aka dakatar sun haɗa da Mista Dio Lamul, mai ba da shawara na musamman kan raya karkara da Mista Moses Sule, jami’in hulɗa da jama’a na mazaɓar Mikang a jihar.
Bere, ya ce dakatarwar ta fara aiki nan take.