✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnan Ekiti ya warke daga coronavirus

Kayode Fayemi ya warke daga COVID-19 bayan kawana 11 a killace.

Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya sanar da warkewarsa daga cutar COVID-19 bayan shafe kawana 11 yana killace.

Fayemi a cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce sakamakon gwajin da aka yi masa na baya-bayan nan ya nuna cutar ta coronavirus ta rabu da shi.

“Bayan kwana 11 a killace na samu labarin cewa sakamakon gwajin COVID-19 da aka sake yi min ya nuna na warke.

“Ina godiya ga Allah sannan iyalaina da likitoci da masu masoya bisa addu’o’in da fatan alheri da kuma goyon bayansu.

“Dole mu ci gaba da yin duk abin da ya kamata domin shawo kan wannan annoba”, inji sakon.