Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya koma jam’iyyar PDP, inda ake sa ran zai yi takarar gwamna karo na biyu a zabe mai zuwa.
Obaseki da dandazon mabiyansa sun isa Ofishin PDP na jihar inda ake taron karbarsa, kwana biyu bayan ya fice daga jam’iyyarsa ta APC, kuma mako guda bayan jam’iyyar ta hana shi tsayawa takara.
Bayan nan ne Aminiya ta kawo rahoton shirye-shiryen jam’iyyar PDP na ganin gwamnan ya koma cikinta inda ta shiga zawarcinsa bayan ficewarsa daga APC.
A ranar Alhamis Kwamitin Gudanarwan PDP ya dage zaben fitar da dan takararsa na zaben gwamnan Edo zuwa ranar 23 ga watan Yuni daga ranar 19 da kuma 20 ga watan.
- PDP ta dage zaben fidda dan takarar Gwamnan Edo
- PDP na zawarcin Obaseki bayan APC ta hana shi takara
- Gwamnan Edo ya fice daga APC bayan ganawa da Buhari
- APC ta hana gwamnan Edo tsayawa takara
Shaidu sun tabbatar wa wakilin Aminiya cewa hakan na daga cikin yunkurin ba wa gwamnan damar yin takara a zaben bayan ya shigo jam’iyyar.
APC ta hana Obaseki tsayawa takara ne saboda zargin da ta yi na wasu alamun tambaya da ta ce akwai a kan takardunsa.
Sai dai ya karyata zargin yana mai cewa da ma ba ya tsammanin samun adalci a zaben muddin dakataccen shugaban jam’iyyar kuma magabacinsa a jihar Edo, Adams Oshiomhole na da hannu a ciki.
Wasu majiyoyi daga APC na cewa kungiyar gawmnonin jam’iyyar na kokarin ganin Obaseki ya dawo ya yi takara a cikinta bayan da kotu ta dakatar da Oshiomhole a ranar Laraba.