Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai, ya sallami mataimakin shugaban kungiyar Kwallon kafa ta Lobi Stars, Mike Idoko daga mukaminsa.
Yayin zantarwarsa da manema labarai a ranar Alhamis cikin birnin Makurdi, Sakataren gwamnatin Jihar, Anthony Ijohor, ya ce sanarwar sallamar Mista Idoko za ta fara aiki ne nan take.
- Kano: Mata na neman rabuwa da miji saboda lalacinsa
- Mun tsiyace, kasafin kudin da ake ware mana ya yi karanci — Majalisa
Sakataren ya ce, matakin sallamar mataimakin shugaban kungiyar kwallon kafar na da alaka da rashin kwazo da kungiyar ke samu a bayan nan.
“Tsige Idoko daga kan matsayin nasa zai fara nan take, an kuma umarce shi da ya gaggauta mika duk wani abu mallakar gwamnati da ke ofishinsa ga sakataren kungiyar kwallon kafa,” in ji shi.
Ijohor ya ce, gwamnan yana kuma godiya ga Mista Idoko kan aikin da ya yi wa Jihar lokacin da yake rike da mukamin nasa, ya kuma yi masa fatan alheri kan samun wata damar a nan gaba.
Rahotonni na cewa, bayan buga wasanni 14, Kungiyar Lobi Stars a yanzu haka tana mataki na 10 a gasar wasannin Najeriya.