Kungiyar Kwallon Kafa ta Lobi Stars da ke garin Markudi a Najeriya, ta bayyana cewar ba ta da sha’awar daukar Cristiano Ronaldo wanda ya raba gari da Manchester United.
Kungiyar da ke garin Markudi a Najeriya, ta sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da fitar a shafinta na Intanet.
- Kotun daukaka kara ta tabbatar da takarar Bwacha a Taraba
- Badakala: Kotun daukaka kara ta rage daurin da aka yi wa Faisal Maina
Sanarwar ta ce: “Mu Lobi muna sanar da cewar ba mu yi wani yunkuri na tuntubar Cristiano Ronaldo ko kuma wakilansa ba.
“Muna masa fatan alheri.”
Yanzu haka dai Ronaldo ya mayar da hankalinsa ne kan Gasar Kofin Duniya da ake bugawa a Kasar Qatar.
Manchester United ta warware alakar da ke tsakaninta da dan wasan bayan wata hira da ya yi da dan jarida Piers Morgans, inda ya caccaki kungiyar da mai horas da ita, Erik ten Hag.