Fadar Shugaban Kasa ta zargi Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai da tunzura jama’a ta hanyar furta kalaman kiyayya masu rura wutar kabilanci.
Hakan na kunshe cikin sanarwar da mai magana da yawun Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu ya fitar ranar Laraba mai bayyana damuwa kan kalaman gwamnan na Benuwai.
- An yi garkuwa da wata mata bayan sa’a 24 da mutuwar mijinta a Katsina
- Ba za mu dauki Ronaldo ba a bazarar nan —City
A cewar Malam Shehu, Ortom na furta kalamai na kabilanci da tunzura jamaa mai kama da wanda ya haddasa kisan kiyashin da ya auku fiye da shekaru 25 a kasar Rwanda.
Shehu ya ce irin haka ce ta kasance a Kasar Rwanda inda jagororin kabilar Hutu suka rika iza jama’ar kasar a tsakanin junansu da cewa akwai wata kitumurmura ta rinjayar da ’yan Kabilar Tutsi a kan sauran.
Malam Shehu ya caccaki ikirarin da gwamnan ya yi na cewa akwai wani tuggu da ake kullawa na rinjayar da kabilar Fulani a kan sauran kabilu a jiharsa da kuma Najeriya baki daya.
Kazalika, ya ce munanan kalaman da gwamnan ya ke yi wani yunkuri ne na fakewa da manufarsa ta juya baya a kan samar da burtalan kiwo ga makiyaya a jiharsa.
Mai magana da yawun Shugaban Kasar ya ce wannan akida da gwamnan ya rika a zahiri manufa ce ta take hakki da dakile ’yancin da dokar kasa ta bai wa kowace kabila, lamarin da ka iya rura wutar rikicin kabilanci a tsakanin al’umma.
A wani shiri da Gidan Talabijin na Channels ya watsa a ranar Talata, Gwamnan ya zargi Shugaban Kasa da rikon sakainar kashi kan irin kashe-kashen da ake zargin Fulani makiyaya da aikatawa da sauran matsalolin tsaro a sassa daban-daban na Najeriya.
A baya bayan nan Ortom ya bukaci gwamanatin tarayya da ta fito fili ta kalubalanci, tare kuma da kama, makiyayan da ke daukar bindigogi kirar AK47.
Haka kuma, rahotanni sun sha ambato Gwamna Ortom yana zargin Shugaba Buhari da mara wa makiyaya baya a kashe-kashen da yake cewa sun yi a jihar ta Benuwai.