Sakamakon gwajin da aka yi wa Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai a bayan nan, ya nuna yana dauke da kwayoyin cutar Coronavirus.
Babbar Sakataren Labarai na fadar Gwamnatin Jihar, Terver Akase ne ya inganta rahoton a ranar Laraba da cewa gwajin da aka yi wa Ubangidan nasa ya nuna ya kamu da cutar ta COVID-19.
- Mai Garin da aka sace a Katsina ya kubuta
- Bakuwar cuta ta kashe mutum 4 a Sakkwato, 24 sun kwanta a asibiti
- Cutar COVID-19 ta yi ajalin mutum 15 a Najeriya, 1,303 sun kamu
Wannan lamari na zuwa ne bayan makonni kalilan da sakamakon gwajin wasu daga cikin hadiman gwamnan na jiki ya nuna sun kamu da kwayoyin cutar.
Sai dai Akase ya ce duk da alamomin cutar basu bayyana a tattare da gwamnan ba, tuni ya shiga kiyaye ka’idodin da mahukuntan lafiya suka shar’anta na karbar magani da killace kai.
Sanarwar ta shawarci dukkanin wadanda suka mu’amalanci gwamnanan cikin ’yan kwanakin da suka gabata da su gaggauta tuntubar wadanda suma suka yi cudanya da su domin su je a duba lafiyarsu domin tabbatar da kamuwarsu da cutar ko sabanin haka.
Mai Magana da yawun gwamnan ya nemi daukacin al’ummar Jihar Binuwai da su ci gaba da kiyaye dokokin da aka gindaya na dakile yaduwar cutar musamman sanya takunkumin rufe fuska da amfani da sunadarin tsaftace hannu da kuma bayar da tazara gami da kaurace wa shiga taron jama’a.
Kazalika, ya karfafi gwiwar al’ummar Jihar a kan kada su yi fargabar zuwa a duba lafiyarsu domin tantancesu a kan kamuwa da cutar, lamarin da ya ce hakan zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar.