Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya ƙaddamar da wani babban kwamitin ƙirƙiro masarautu da gundumomin hakimai a jihar.
An ƙaddamar da kwamitin ne a wani mataki na magance buƙatu da dama daga al’ummomi daban-daban da kuma inganta al’adu da tsarin mulki na asali a faɗin Jihar Bauchi.
- Abba ya naɗa Ahmed Musa a matsayin Babban Manajan Kano Pillars
- An gano wasu bama-bamai 56 da ISWAP suka binne a Borno
Gwamna Bala ya shaida wa kwamitin da ya sake duba buƙatu na samar da sabbin masarautu a faɗin jihar.
Ya ce, aikin kwamitin shi ne inganta harkokin gudanar da mulki na cikin gida da inganta al’adu da kuma ƙarfafa muhimmiyar rawar da sarakuna ke gudanarwa wajen haɗin kai da ci gaba.
Gwamnan ya bayyana matakin a matsayin alƙawarin da gwamnatinsa ta yi na tabbatar da adalci da haɗa kai da kuma ƙarfafa tsarin mulki da ci gaba a Jiha da ƙananan hukumomi.
Ya bayyanawa kwamitin da ya ba da shawarar al’ummomin da suka cancanta na sabbin masarautu, da ba da shawarar tsarin gudanarwa don ingantaccen aiki na sabbin masarautu, masarautu ko gundumomi da gabatar da cikakken rahoto tare da shawarwari masu dacewa cikin makonni takwas.
Gwamnan ya buƙaci kwamitin da ya gudanar da aikinsa cikin gaskiya da himma da kuma adalci.
Ya bayyana cewa, shirin na cika alƙawuran siyasa ne da nufin karkatar da hukumomi don samar da ingantattun ayyuka da kuma ƙara rarraba albarkatu.