Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya warke daga cutar coronavirus bayan an fitar da sakamakon gwajinsa a karo na biyu.
Gwamnan ya yi fiye da mako biyu yana jinya, tun ranar 24 ga watan Maris gwajin da aka yi wa Gwamnan ya nuna yana dauke da cutar Coronavirus.
Da maraicen ranar Alhamis ne Gwamna Bala Muhammad Kaura, da kansa ne ya sanar da cewa gwajin da aka yi masa yanzu bai dauke da cutar, kamar yadda ya sanar a shafinsa na Twitter.
- ’Ya’yan gidan Sarautar Saudiyya 150 sun kamu da Coronavirus
- Sakon Gwamnan Bauchi daga inda yake killace
- Gwamnan Bauchi ya kamu da Coronavirus
Gwamnan ya godewa masoyansa da suka saka shi a cikin addu’a lokacin da yake jinya. Sannan ya yaba da kokarin Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa NCDC tare da shugabannin addini na cikin jihar da wajen jihar.
Alhamdulillah. I just received the green light. My second test for #COVID19 returned negative. I thank you all for your prayers & support even while I was in isolation. Most importantly, all the praises & thanks be to Allah – the Most Beneficent, the Most Merciful. #GreaterBauchi
— Senator Bala A. Mohammed (@SenBalaMohammed) April 9, 2020