Gwamnan Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya miƙa yara uku da aka sace daga jihar aka sayar da su a Jihar Anambara ga iyayensu.
Yaran da wasu suka sace an dawo da su ne ta hanyar haɗin gwiwa ’yan sanda a jihohin biyu.
Gwamnan ya yaba da ƙoƙarin gwamnan jihar Anambra tare da matarsa da rundunan ’yan sandan jihohin biyu wajen ƙwato yaran da aka sace.
Ya buƙaci iyaye da su kasance masu lura da kuma kula da lafiyar ’ya’yansu a matsayin babban nauyi, sannan ya yi alƙawarin ɗaukar ƙwararan matakan shari’a a kan waɗanda ake zargin domin su girbi abin da suka shuka.
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Samun Wadataccen Abinci
- An kai hari Fadar Shugaban Ƙasar Chadi
- Nan ba da jimawa za a ƙara kuɗin kiran waya da data — Gwamnati
Gwamna Bala ya ce gwamnati za ta aika da ƙudirin doka ga majalisar dokokin jihar don tabbatar da cewa daga yanzu za a rubuta bayanan duk masu zama a gidajen haya.
Ya kuma yaba wa jami’an tsaro kan rawar da suke takawa wajen magance irin wadannan miyagun ayyuka.
Da yake jawabi ga iyaye, gwamnan ya bukace su da su ci gaba da sa ido tare da tabbatar da tarbiyyar ’ya’yansu da kuma kula da su yadda ya kamata. Ya yi kira ga shugabannin al’umma da su rika sa ido tare da sanya ido ga mazauna yankunansu don hana afkuwar lamarin nan gaba.
Da yake nanata mahimmancin adalci, Gwamna Mohammed ya jaddada cewa jinkiri wajen yanke hukunci shi ne rashin adalci, yana mai ba da umarnin a hukunta masu laifi bisa ga doka.
Da yake miƙa yaran, kwamishinan ’yan sandan jihar Bauchi Auwal Musa Mohammed, ya bayyanawa gwamnan nasarar da aka samu na ceto mutanen.
Iyayen yaran da aka sace sun bayyana godiya ga gwamnan bisa ƙoƙarinsa na ceto yaran da mayar da su gida.