Gwamnana Jihar Bauchi, Bala Mohammed, a ranar Alhamis ya jagoranci dimbin jama’a domin yin Sallar rokon ruwa saboda karancin ruwan saman da Jihar ke fsukanta.
Jim kadan bayan idar da sallar, Gwamnan ya ce Jihar na fama da matsanancin fari yayin da damina ta lula, inda ya ce ya zama wajibi a yi sallar don neman taimakon Allah.
- Har yanzu Najeriya ta fi kowacce kasa arhar man fetur a nahiyar Afirka – IPMAN
- Gobara ta kone shaguna 10 a Kasuwar Rimi da ke Kano
Ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da addu’ar domin manoma su sami damina mai albarka ta yadda za su sami amfani mai yawa.
Gwamnan, wanda ya samu wakilcin Mataimakinsa, Auwal Jatau, ya kuma gode wa Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu da sauran malaman Jihar saboda shirya sallar.
Bala Mohammed ya kuma bukaci jama’ar Jihar da su goyi bayan manufofin gwamnatinsa, inda ya ce sun samar wa manoma takin zamani da sauran kayayyakin amfanin gona.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito cewa kusan tsawon mako guda ke nan, shugabannin al’umma da na addini suna shirya rokon ruwan domin neman agajin Ubangiji.
Mataimakin Babban Limamin Babban Masallacin Bauchi, Ahmad Auwal Na’ibi. (NAN)