✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Zulum ya zabi sabon Sarkin Biu

Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum, ya amince da nadin Mai Mustapha Umar a matsayin sabon Sarkin Biu. Sabon Sarkin shi ne zai gaji Mahaifinsa, marigayi…

Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum, ya amince da nadin Mai Mustapha Umar a matsayin sabon Sarkin Biu.

Sabon Sarkin shi ne zai gaji Mahaifinsa, marigayi Mai Umar Mustapha wanda ya koma ga Mahaliccinsa a ranar 16 ga watan Satumba.

A yayin da ake gabatar da wasikar nadin ga sabon Sarkin a ranar Litinin, Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Usman Jidda, ya taya shi murnar kasancewarsa zabin majalisar masu zaben Sarki.

Mataimakin Gwamnan Jihar, Hon. Usman Umara Khadafur, shi ne ya gabatar da wasikar nadin ga sabon Sarkin a gaban majalisar zaben Sarki a fadar Sarkin Biu.

Yayin da Mataimakin Gwamnan ke gabatar da wasikar nadin