✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna ya tsawata wa malaman makaranta a Jigawa

Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Badaru Abubakar ya nuna bacin ransa ga malaman makarantun firamare a jihar saboda rashin koyarwa yadda ya kamata da suke yi…

Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Badaru Abubakar ya nuna bacin ransa ga malaman makarantun firamare a jihar saboda rashin koyarwa yadda ya kamata da suke yi a makarantun jihar.

Gwamnan ya nuna haka ne a yayin da yake gabatar da jawabin a wajen taron masu ruwa-da-tsaki a bangaren ilimi, a dakin taro na Sa Ahmadu Bello da ke Sabuwar Sakatariyar Jihar.

Ya nuna takaicinsa game da yadda malaman makarantun firamare ba su tsayawa a kan aikinsu na koyarwa a daukacin makarantun jihar. Ya ce da yawa wadansu malaman alfarma ce ta ba su damar koyarwa a makarantun, ba cancanta ba

Saboda haka Gwamna Badaru ya hori kansiloli su dauki mataki a kan malaman makarantun ta hanyar tona asirin duk malamin da ba ya zuwa aiki ko yake sakaci da aikinsa.

Kuma ya hori kansilolin su guji yin aiki da son zuciyarsu. “Kada mutum ya yi amfani da damarsa wajen cin zarafin wani,” inji shi.

Ya  bukaci kansilolin su ji tsoron Allah dangane da bayar da sahihan bayanai a kan malaman makarantar. Ya gargade su da su yi amfani da matsayinsu wajen yi wa malaman makarantar nasiha saboda su rika tsayawa a kan aikinsu.

Daga nan sai Gwamna Badaru ya nuna damuwarsa game da rashin dangantaka mai kyau a tsakanin kansiloli da ciyamomi da mataimakansu da sauran ma’aikatan kananan hukumomi a fadin jihar ta Jigawa. Saboda haka ya bukace su da su yi iyakacin kokarinsu wajen dinke baraka a tsakaninsu saboda a samu zaman lafiya, a daina yin gaba da juna.