Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi, ya ba da umarnin kama wadanda suka dafa abinci mara dadi yayin wani shagali na Kirsimeti ga zawarawa a jihar ranar Alhamis.
Gwamnan, wanda bai bayyana sunan wanda ya dafa abincin ba, ya ce abin takaici ne a ce mutum ya ba wasu abin da ya san shi ba zai iya ci ba.
- Croatia ta doke Maroko a neman mataki na 3 a Gasar Cin Kofin Duniya
- Sojoji sun kashe ’yan ta’addan Boko Haram 6 a Borno
Ya ce ’yan sanda za su bi duk matakin da ya dace wajen bincike kan lamarin, don ganin wacce ake zargin ta dawo da kudaden da aka ba ta wajen shirya abincin.
A cewar Gwamnan, “Saboda haka, za mu sake shirya irin wannan taron a karo na biyu don girmama iyayenmu. Littafin Bibul ya koya mana girmama iyayenmu saboda rayuwarmu ta yi albarka.
“Kuma ni da kaina zan sake duba yadda za a dafa abincin a taro na gaba da za a gudanar ranar 21 ga watan Disamba mai zuwa.
“Tuni ma na ba Mataimakina da mai taimaka min kan harkokin addini da walwalar jama’a umarnin yin duk tsare-tsaren da suka kamata.
“Za a yi bikin ranar 21 ga watan Disamba, kuma duk wanda ya yi kokarin yin ba daidai ba ga wadannan mutanen to tabbas ya dauko Dala ba gammo,” inji Gwamna Umahi.