Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta kara wa jihar kason kudi domin yaki da jahilci hakan ya taimaka wa kokarin da take yi a harkar bunkasa ilimi.
Gwamna Atiku Bagudu ya yi wannan kira ne lokacin da yake jawabi wajen bikin Ranar Yaki da Jahilci ta Duniya ta kasa da aka gudanar a Birnin Kebbi.
Sanata Atiku ya ce bikin ya zo daidai lokacin da ya kamata inda ya nuna ji dadinsa kan yadda aka zabi jihar a bana domin gudanar da taron na wuni biyu.
Gwamnan ya ce idan Gwamnatin Tarayya ta kara musu kason kudin a shirye gwamnatinsa take ta yi tsayin daka wajen yaki da jahilci da kuma hada hannu da masu ruwa-da-tsaki wajen yaki da jahilci da kuma ganawa da jama’a domin nuna musu muhimmancin neman ilimin addini da na zamani domin rage jahilci a cikin jama’a.
Gwamnan ya ce ya zama wajibi gwamnatin jihar da Hukumar Ilimin Bai-daya ta kasa su tashi tsaye domin yaki da jahilici a tsakanin jama’a, kuma ya yi kira ga gwamnatoci a dukan matakai da cibiyoyi da kungiyoyi masu zaman kansu su hada hannu domin samun nasanar wannan shiri.
A jawabin Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu wanda Babban Daraktan Ilimin Bai-daya Mista Jonathan Mbaka ya wakilta, ya ce kimanin kashi 65 zuwa 75 na mutanen kasar nan ne suke fama da jahilci, inda ya ce abin takaici ne. Ya ce ilimi shi ne kashin bayan ci gaban kowace kasa, saboda haka ya yi kira ga masu ruwa-da-tsaki su shigo su ba da tasu gudunmawa domin kawar da jahilci a cikin al’umma.
Ministan ya gode wa Gwamnatin Jihar Kebbi kan bunkasa harkokin ilimi, kuma ya bukaci ta kara matsa kaimi wajen yaki da jahilci a cikin al’umma.
Babban Sakataren Hukumar Ilimin Manya, Farfesa Abba Abubakar Haladu, ya ce addinan Musulunci da na Kirista suna koyar da mabiyansu muhimmancin ilimi, in da ya yi kira ga jama’a su yi amfani da damar da gwamnati ta samar masu ta fuskar neman ilimi domin raya kasar nan.
Sakataren ya bukaci masu hannu da shuni su yi koyi da matar Gwamnan Jihar Kebbi Hajiya A’isha Bagudu wadda take ba da gagarumar gudunmawa domin kawar da jahilci a cikin jama’a, inda ta kafa wata gidauniya mai suna Mallapai domin karfafa wa mata da matasa da kuma hana yin barace-barace.
Abubakar Halidu ya ce kuma ta bude makarantu da cibiyoyin koyar da sana’oi don taimaka wa marasa galihu su koyi sana’o’in hannu domin dogaro da kai da kuma yakar jahilci saboda kauce wa zaman kashe wando a tsakanin marasa galihu.