Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya yi afuwa ga fursunoni aƙalla goma sha biyu a gidajen gyaran hali guda biyar da ke jihar.
Gwamnan ya yi hakan ne a wani ɓangare na murnar bikin cika shekaru 64 da samun ‘yancin kan Nijeriya da kuma shekara 28 da kafuwar Jihar Nasarawa.
Gwamna Sule wanda ya ‘yantar da fursunonin a cibiyoyin gidajen yari da ke Lafia, babban birnin jihar, ya gargaɗe su da su ɗauki izina da zaman da suka yi a gidan gyaran hali, domin su ci gaba da amfanar da kansu da kuma al’umma baki ɗaya.
- Kotu ta ba da belin tsohon Gwamnan Taraba kan N150m
- Adadin waɗanda suka mutu a haɗarin kwale-kwalen Neja ya ƙaru zuwa 24
Gwamnan ya taya Kwanturolan gidan gyaran hali na jihar murnar samun nasarar kula da al’amuran gidajen yari a jihar, tare da taya fursunonin murnar cikar Nijeriya shekaru 64 da samun ‘yancin kai da kuma murnar cikar Jihar Nasarawa shekara 28 da kafuwa.
Kazalika, ya yaba da ƙoƙarin da fursunonin suka nuna wajen koyon sana’o’in hannu a yayin da suke zaman gidan ɗan Kande.
Sai dai ya bayyana cewa baya ga ƙudurin inganta jin daɗinsu, ya kuma yi alƙawarin magance wasu matsalolin da cibiyar ke fuskanta.
Da take zayyana matsayin gidajen yarin musamman a fannin walwalar fursunonin, Babbar Alƙalin Jihar Nasarawa, Mai Shari’a Aisha Bashir Aliyu ta bayyana cewa, ɓangaren shari’a zai ci gaba da yin iya ƙoƙarinsa wajen ganin cewa babu cunkuso a cibiyoyin gyaran hali da ke jihar.
A nasa ɓangaren, Babban Lauyan jihar, Barista Labaran Magaji ya bayyana cewa, afuwar da aka yi wa fursunonin 12 ya yi daidai da tanadin tsarin mulki wanda ya bai wa kwamitin jin ƙai na jihar damar gudanar da ayyukan ‘yantar da fursunonin da ke zaman gidan yari daban-daban.