Gwamnatin Jihar Kogi ta nesanta Gwamna Usman Ododo da zargin da hukumar EFCC ke masa na tserewa da tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello, a lokacin da jami’an hukumar suka je gidan tsohon gwamnan da ke Abuja domin kama shi.
Kwamishinan yada labaran jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ne ya bayyana hakan yana mai cewa Gwamna Ododo mutum ne da ya tsaya kai da fata wajen bin doka da oda.
A hirar da gidan talabijin na Channels ya yi da shi, Fanwo ya kara da cewa zargin da EFCC ke wa Gwamna Ododo ba shi da tushe balle makama.
A cewarsa, gwamnan jihar, “bai taimaka wa tsohon gwamna Yahaya Bello wajen tssrewa daga gidansa ba.
“Wannan zargi ba shi da tushe kuma hukumar ta yi shi ne domin cim ma wani burinta.”
Fanwo ya musanta zargin da EFCC ke wa Gwamna Ododo na kare hana hukumar kama Yahaya Bello, yana mai kafa hujja da hukuncin wata babbar kotu da ta hana hukumar musguna wa tsohon gwamnan.
“Babu wnada Yahaya Bello ke guje wa, umarnin kotu ya kare masa ’yancinsa na dan Adam,” inji kwamishinan.
Daga nan ya soki hukumar yana mai kalubantarta ko tana da tabbaci game da ainihin inda Yahaya Bello yake.