Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ya kara nada sabbin hadimai 250, don taimaka wa gwamnatinsa wajen gudanar da ayyuka.
Darakta-Janar na harkokin siyasa na gwamnatin jihar, Mikailu Aliyu ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai na Laraba a Gusau, babban birnin jihar.
- Mahara sun kashe mutum 2 a wurin taron APC a Enugu
- Wutar lantarki ta babbake barawon wayar transfoma
Mista Aliyu ya ce nadin sabbin hadiman wani yunkuri ne na tabbatar da cewar ayyuka sun cimma lungu da sako na al’ummar jihar.
Ya ce tun bayan kafa gwamnati, Matawalle ya nada kwamishinoni 25, masu ba da shawarwari na musamman 55, Darakta-Janar 72 da kuma mambobin gwamnati 12.
Ya ce nade-naden hadiman na yanzu sun hada da sabbin Darakta-Janar takwas, karin masu ba da shawarwari na musamman 242, lamarin da ya kawo adadin hadiman gwamnan suka zama 1,700 ke nan.
Kazalika, Mista Aliyu ya musanta rade-radin da ke cewar Gwamna Matawalle na shirin ba da umarnin cafke Shamsu Shehu, shugaban masu amfani da kafafen sada zumunta na Karamar Hukumar Marafa, inda ya ce labarin ba shi da tushe balle makama.
Aliyu, ya ce gwamnan jihar, mutum ne mai ba wa kowa damar fadar albarkacin bakinsa musamman ga abubuwan da suka shafi sha’anin siyasa.