✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Masari ya rattaba hannu kan hukunci kisa ga masu garkuwa

Gwamna Jahar Katsina Aminu Bello Masari ya sanya hannu a kan gyaran dokar kundin Shari’ar “Penal Code” domin tsayar da hukuncin da ya dace a…

Gwamna Jahar Katsina Aminu Bello Masari ya sanya hannu a kan gyaran dokar kundin Shari’ar “Penal Code” domin tsayar da hukuncin da ya dace a kan laifukan da kundin bai yi magana ko kunsa a cikinsa a baya ba. Sanya hannu a kan wannan dokar ya tabbatar da hukuncin kisa a kan duk wanda kotu ta sama ta kuma tabbatar da laifin yin garkuwa da mutane da kuma waɗanda aka samu da laifin satar shanu.

Haka kuma an tanadar da hukuncin daurin rai da rai hade da biyan tara ga duk wanda kotu ta samu kuma ta tabbatar ya aikata fyade, sannan kuma mai laifin zai biya diyya ga wadda aka yi wa laifin. Ita dai wannan doka ta zo daidai da lokacin da Jahar take fuskantar matsalar tsaro a yankunan ƙananan hukumomin Jibiya, Batsari, Safana,Ɗan Musa, Ƙanƙara, Faskari har zuwa Sabuwa.

Matsalar garkuwa da mutane da kuma kisan jama’a barkatai ya ta’azzara musamman a yankin Ƙaramar Hukumar Batsari a inda ƙasa da kwana 7 anyi asarar rayuka sama da mutum 50 daga garuruwa. Kusan kisan ba gaira ba bu dalili na son rinjayar sata tare da yin garkuwar don neman kuɗin fansa. Kisa na baya-bayan nan shine wanda aka yi a ƙauyen Ƴargamji da ke hanyar Batsari zuwa Jibiya a cikin Ƙaramar hukumar ta Batsari inda aka kashe mutum 18. Gawarwakin da aka dauko aka kawo wa Gwamna Masari da Maimartaba Sarkin Katsina Dokta Abdulmuminu Kabir. An kuma birne su a maƙabartar Ɗantakun da ke cikin garin.