✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Gaidam ya kalubalanci ’yan siyasa

Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya kalubalanci masu rike da mukaman siyasa da zababbun wakilan jama’a a jiha da tarayya aga jihar su yi…

Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya kalubalanci masu rike da mukaman siyasa da zababbun wakilan jama’a a jiha da tarayya aga jihar su yi kokarin inganta rayuwar al’ummar da suka zabe su ta hanyar gudanar da ayyukan raya kasa da samar da kayan koyon sana’o’i don samar da aikin yi ga matasa.
 Gwamna Gaidam ya bayyana hakan ne ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin siyasa da majalisa Alhaji Mai Mala Buni a lokacin da yake jawabi yayin kaddamar da wasu kayayyakin koyon sana’o’i da suka hada da kekunan dinki da na koyon kanikanci da sauransu da kudinsu ya kai Naira miliyan 98 da dan majalisar Wakilai na Mazabar Gaidam/Yunusari/Bursari, Alhaji Goni Bukar ya samar ga jama’arsa a garin Dapchi hedikwatar karamar Hukumar Bursari.
 Alhaji Ibrahim Gaidam ya ce abin da dan majalisa ya yi, ya dace kuma ya zo a daidai lokacin da ake bukata ganin al’umma na cikin kunci sakamakon tabarbarewar harkokin tsaro a jihar.
Tun farko a jawabin Alhaji Goni Bukar ya ce ya fara wannan aiki ne ga al’ummarsa don kawar da talauci da ke addabar jama’a, tare da sauke nauyin da ke kansa.
 Sai ya hori wadanda suka ci gajiyar kayayyakin su yi amfani da su ta hanyoyin da suka dace don su samu dogaro da kansu, su kuma guji sayar da su.