✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamna Finitiri ya yi alhinin mutuwar mahaifiyar Sanata Binani

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, ya jajanta wa Sanata Aisha Dahiru Binani dangane da rasuwar mahaifiyarta, Hajiya Utiya Dahiru Chiroma wacce mai yankan kauna…

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, ya jajanta wa Sanata Aisha Dahiru Binani dangane da rasuwar mahaifiyarta, Hajiya Utiya Dahiru Chiroma wacce mai yankan kauna ta katse mata hanzari a ranar Alhamis bayan ta yi ’yar takaitacciyar jinya.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Fadar Gwamnatin Jihar Adamawa, Humwashi Wonosikou ya fitar a ranar Juma’a.

Gwamna Fintiri wanda ya yi addu’ar Allah ya baiwa Sanata Aisha hakurin rashin da ta yi, ya kuma mika ta’aziyyarsa ga sauran ’yan uwa da makusantan marigayiyar.

A cewarsa, “Mama ta yi rayuwa ta rikon amana da gaskitya tare da hidimtawa al’umma.

Ya kuma yaba wa marigayiyar dangane da kyakkyawar tarbiya da ta baiwa ’ya’yanta, lamarin da ya ce hakan zai sa su zama ’yan kasa na gari kuma babu shakka ta bar baya mai kyau.

Sanata Binana mai wakilcin shiyyar Adamawa ta Tsakiya a zauren Majalisar Dattawa, ta rasa mahaifiyarta ne a ranar Alhamis kuma an yi jana’izarta a ranar Juma’a bisa tanadin addinin Islama.